SHARRIN ZINA KAFIN AURE
Duk wanda yayi zina da wata cikin soyayyah, kokuma tayi zina da wani cikin Soyayyah to jarrabawa na farko da zai fara zuwa musu shine son Aure tsakaninsu, especially ma idan ba mutanen banza bane dama, amma idan namiji mutumin banza ne, lokacin da yasamu kanki yayi zina dake to zakiga yana ja baya dake, ma'ana yasamu abinda yakeso, haka kuma idan mace mazinaciya ce idan ta baka kanta kukayi zina, to lokacin da kukayi na farko, maimakon kuji tsoron Allah kada ku sake, zakaga tanaso kuyitayi, amma bazata furtama tanaso kuyitayi ba, saidai idan kuka keɓe zata cemaka nikam kamin koda kaɗanne, to dama shi namiji mutum ne mai amfani da damar daya samu. Idan kuma mace bata zama haka ba, to abinda takeyi shine lokacin da kukeyin waya zatayita nuna wallahi jiya baka fita kaina ba, naso kayita mini, Subhan Allah!
Babban sharri da aikata zina yake jawowa shine, idan ka aikata shi bayan kasan kuskurene wataƙila ma ka tuba, to koda kafi kowa aikin Alkhairi dole sai an sakaka a wuta ta cire wannan fitina kafin a shigar dakai Aljannah, saidai ya danganta da tsakaninka da imaninka da Allah, idan bayan tubanka kasamu shiriya wajen ibada yadda ya kamata, to Allah yana iya sakaka a wuta kamar ƙibtawan idanu, idan kuma ba haka ba, yana iya sakaka a wuta kamar tsawon yadda imaninka da tubanka ga Allah yake, shiyasa zakaji Maluma sunacewa kayi riƙo da istigafari har iya lokacin da kaji a ranka kamar Allah ya gafarta maka, ma'ana dai ba'a shiga Aljannah da dottin zina. Sharri na gaba kuma shine, duk wanda ya aikata zina dole sai tayi tasiri a samunsa, wataƙila yagama kasuwanci kafin yabar duniya ya talauce, kokuma ya rage ƙarfin Arziƙi da Allah ya tsara zai bashi, kokuma kaganshi kullum cikin nema amma bayida nitsuwa cikin abinda yasamu, ma'ana zakaganshi baya iya taimakon hatta iyayensa ko iyalensa, amma da zaran karuwansa ta nema zakaga cikin rawan jiki zai bata, wa'iyazu billah!
Sai sharri na gaba shine, idan mutum ya aikata zina to bazata faɗi ƙasa banza ba, dole saiya samu cikin iyalensa, kokuma ƙannen sa especially mata, kokuma jikokinsa, dole dai sai wani ya ɗaukoshi wajen aikata irin wannan sharrin. Saidai idan shine yayita Addu'an Ya Ubangiji kada ka bari nazama silan ɓatanci ga iyalaina ko ƙannena, kokuma jikokina. To idan yayi dace zata iya ƙarewa kansa shi kaɗai. Kuma wallahi ita zina koda sau 100 ne kayi, lokacin daka daina ka taimaki kanka, saboda tabbas Allah zai karɓi tubanka, sannan kuma shigan zunubinta gareka zai tsaya, ma'ana idan kanayi ba kamar sauran zunubai bane, ita idan kullum kayi zunubi ake tara maka.
Ƴan'uwa wallahi idan mutum yana zina sai ya tuba tuba mai kyau, to wallahi zaiga yana ci gaba, kuma zai samu nitsuwa a ransa, sannan kuma zaigane tabbas Allah masoyinsa ne, saboda zaiga duk wani Alkhairi yana kusantarsa! Yaa Ubangiji ka ƙara karemu da aikata zina, ka wanke mana zukatanmu, sannan kayi mana tsari da faɗawa cikinta, Ameen.