TUNANINKA, HANYAR MALLAKAR DIMBIN KUDADE.
(KASHI NA UKU)
-KU KARANTA Labarin Mutanen Da su ka Sami Dimbin Kudade Saboda Amfani da Tunaninsu a Aikace.
MARCONI
A lokacin da Marconi ya shelantawa duniya ya kirkiro ilimin da za a iya isar da sako ta iska, dariya abokanensa su ka rika yi masa. Kai, har Asibiti aka kai shi, aka ce a duba kwakwalwarsa saboda ana tunanin ya sami tabin hankali. To amma a yau ga sakamakon aikin Marconi nan, muna gani a Talabijin, Rediyo da wayar Selula.
MACDONALD
Ray Kroc wani mutum ne wanda tunaninsa ya amfane shi. Wani mutum ne da ke sana'ar sayar da Madara. Yana da masu sayen madararsa a tsakanin mutane daidaiku da wuraren sayar da abinci.
Watarana ya sami odar sayen Madara galan takwas daga wani wajen sayar da abinci a San Bernardino a birnin California. A ranar ya yi tunanin ya kamata ya je da kan sa wurin sayar da abincin saboda ya ga yadda su ke sayar da madarar da su ke saya a wurinsa. A lokacin da ya je, ya lura wurin cin abincin mai suna Macdonald ya fi dukkanin ire irensa a birnin yawan masu zuwa sayen abinci. Bayan dogon nazari da ya yi, ya fahimci za a iya samun riba a cikin irin wannan sana'a, da kudi masu yawa. Saboda haka ya yi tunanin ya bude reshen irin wannan don sayar da abincin.
Bai bata lokaci ba, ya tuntubi wanda ya mallaki wurin mai suna Macdonald ya gabatar masa da bukatars. Shi ma ya yarda da bukatar da aka gabatar masa.
Bayan shekara daya, sai da Macdonald ya wuce maganar wurin sayar da abinci, ya koma babbar Ma'aikatar samar da abinci iri daban daban. Daga karshe shi ne ya sayi Macdonald ya canza shi zuwa babban Kamfani a duniya, kuma ta sanadin haka ya zama kasurgumin mai kudi. A yanzu za ku iya ganin cubiyoyin Macdonald a ko'ina a duniya.
A yanzu fa duniya cike take da hanyoyin samun dimbin kudade, wadanda mutanen da su ka gabata ba su sami irin damarmakin ba. A domin haka, idan tunani ya shiga kwakwalwar mutum shi kenan. Amma fa a gane, babu wata nasara da ake samu da tunani idan akwai mutuwar zuciya, yanke kauna da ragwanci.
Babu cigaba, ba samun dimbin kudade a duniyar yanzu ga masu hasashe kawai suna zaman babu motsi da yi a aikace. Idan aka karanta tarihin wadanda su ka yi nasara a rayuwarsu har su ka zama abin misali, za a ji yadda su ka yi ta fadi tashi, wahala da sadaukarwa da karfin hali kafin su kai ga samun nasara.
JOHN BURRYAN
Bayan da aka kama shi saboda ra'ayinsa na addini, a cikin gidan Fursuna ya rubuta wani littafi mai suna ' The Pilgrim's Progress'.
O. Henry:
Bai taba sanin yana da wata baiwa ba sai bayan da kaddara ta fada masa, aka kama shi aka kai gidan fursunan birnin Columbus ta jihar Ohio a kasar Amurka. Saboda matsin da ya shiga, sai ya gano ashe yana da wata baiwa wadda idan ya yi aiki da ita, zai iya zama mai kudi na halas, a maimakon yadda ya dauki kansa a baya matsayin mai aikata laifuka. Hakan na nuna matsi na rayuwa na iya nunawa mutum wata baiwa da Allah ya ba shi, wadda yana iya amfani da ita ya sami waraka kuma ya tara dukiya ta halas.
EDISON.
Shi ne fitaccen mutum a duniya wajen kwarewa a fagen kirkire kirkire na kimiyya. Kafin lokacin sana'arsa ita ce aikin sarrafa wayar tangaraho. A sanadin haka ya gano ashe dai yana da wata baiwa wadda ya yi aiki da ita, kuma har ya yi fice a duniya.
HELEN KELLER:
Mace ce da aka haife ta makauniya, bebiya ba ta san kowa ba. Amma yanzu sunanta ya shiga cikin kundin tarihin duniya. Rayuwarta darasi ne da ke nuni cewa 'Babu rashin nasara ga kowa, sai idan mutum ya bawa rashin nasarar dama.
Mun kammala wannan Babin.
Shin kun san cewa, Sallamawa, Soyayya da Jima'i suna kaifafa tunani wajen nazarin hanyoyin samun kudi?
Mu hadu a gobe Insha Allah domin jin cikakken bayani.
Daga BINCIKEN
Bala M Makosa
(Baban Haidar).
Allah ya ba mu yini lafiya.