AUREN DOLE HARAMUN NE
Wani Dottijo ne yacewa matarsa ta bashi ruwa a buta zaiyi Alwala, to kafin ya fara Alwalan saiya fara dariya, yayita dariya sosai, sai matarsa tace, maigida lafiya? Menene yabaka dariya haka? Saiyace mata wallahi na tuna lokacin lokacin da za'a mana Aure fa bakyaso! Shine abunda yabani dariya.
Saitayi Murmushi tace, ai maigida har yanzu bana sonka, kullum idan kazo fita daga gida sai nayi addu'a Allah yasa kada ka dawo😳
A wannan lokacin kuma yakai shekaru kusan 65 ita kuma takai shekaru 45, bayan ta furta wannan maganar sanda butan ya faÉ—i a hanunsa, kuma suna da yara dayawa a wannan lokacin, sannan kuma yayine da wasa, tace masa babu lokacin da zai fita fashe saitayi addu'an Allah yasa yayi hatsari, kokuma tanaso taji labarin ya mutu, Subhan Allah!
Lokacin da aka musu Aure batason shi, tabbas idan mace bata sonka, wallahi karka Aureta, domin zata iyayin komai, Allah ya tsaremu.