JAHOHI 10 na Nageriya tare da yadda aka samu Asalin Sunayensu

.


1- ABIA- jahar ta samu sunanta ne daga sunayen wasu MANYAN jinsin kabilun jahar 4 wato:

A- Aba

B- Bende

I- Isuik

A- Afikpo

.

2- KADUNA- jahar ta asamu asalin sunanta ne daga Sunan Dafbar  ruwa "Kada", wato ajumulance idan kafadi Sunayensu a hausa  zai baka Kadunas, kasancewar Kaduna gari ne Mai tarin tafkunan ruwa awancan lokacin

.

3- ADAMAWA- jahar ta samu sunanta ne daga Sunan wani jarimi da jahar tayi a tarihi mai suna Maddibo Adama bin Hassan alokacin da ya mamaye yankin akarni na 19

.

4- KANO- jahar ta kano itama ta samu Asalin Sunan tane daga wani makeri mai fasa Duwatsu da yayi zamannin a garin Gaya 

.

5- KATSINA- jahar ta samu sunanta ne daga matar wani sanannan Basarake da yayi zamaninsa awancan lokacin mai suna Janzama

.

6- JIGAWA- jahar jigawa dai jaha ce da Allah (s.w.a) ya huwace mata da kasa da ke dauke da tsaunikan Dawatsu kala kala, kuma jahar ta samu suna ne sakamakon wannan Jigagin da take dauke dashi na kasa da Duwatsu

.

7- LAGOS- jahar ta samu sunan ta ne daga wata kallar turawan mulkin mallaka na kasar Portugal wato ' ' 'Likes' da kuma kalmar 'Lagoon' Wanda duk kalmomin suna nufin Tafkin ruwa, tarihi ya nuna tun cikin Shekara ta 1472 turawan na Portugal suka fara zama a yankin

.

8- YOBE- jahar Yobe ta samu sunanta ne daga wani kogin da ake Kira Waube ko Ouobe ko kuma kogin Yo Wanda yanzu haka shi ake Kira da Komadugu Yobe


9- ONDO- jahar itama ta samo Asalin sunanta ne daga wasu fatake da zukayi zamani awancan lokutan da ake kiransu da "Ondo" har suka kafa masarautar da ake kira da Ondo Empire

.

10- NASARAWA- kalma ce ta nasara kuma ta samu asalin sunanta daga wani Babban Basarake da yayi gwagwarmaya Mai suna Makama Dogo

.

Menene Ra'ayin ka ki?